6 Satumba 2026 - 21:59
Source: ABNA24
Iran: Ta Kara Farashin Man Fetur A Ƙasar

Mai magana da yawun gwamnati ta sanar da cewa farashi na katin mai wand aba kason gwamnati ba zai ƙaru zuwa Toman 10.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Fatemeh Mohajerani, mai magana da yawun gwamnati, a cikin wani saƙon bidiyo ta sanar da cewa: "Farashin katin mai daga safiyar ranar 11 ga Satumba zai ƙaru zuwa Toman 10."

Ta ce: "A cikin tarurrukan ƙwararru masana an kawo adadi daban-daban, amma tun da shugaban ƙasa ya yi alkawari ga jama'a, an kayyade shi a iya Toman 10.

Mohajerani ta kara da cewa: " a kason gwamnati Lita 60 na man fetur a Toman 1500 kuma lita 50 na man fetur a Toman 3,000 har yanzu ba su canja ba."

Mai magana da yawun gwamnati ta ci gaba da cewa: "Ƙaruwar farashin katin mai za ta taimaka wa rayuwar jama'a."

………….

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha